Yadda ake gane lafiyayen ɗa namiji domin ma:aurata zallah – malama Juwairiyya


A wajen karatu malama Juwairiyya usman suleiman tayi jan hankali da nasiha kan yadda ake gane lafiyayen da namiji tun daga yarinta har ya girma wanda malamar ta lissafo abubuwa wanda tabbas iyaye su kula da diyansu akan wannan siffofin,. Malam tayi wannan furucin ne akan wani dan gajeren bidiyo da
 maryam revenge ta wallafa a shafin ta na tiktok.

Malamar tayi wannan maganar ne a lokacin take majalisi na wa’azi inda take gayawa uwaye mata cewa tayi wannan zancen kuma zata sake fadi a lokacin da take koyawa iyaye mata su kula da lafiyar ƴaƴansu tun suna goyonsu.

” Idan kina goyon da namiji ko wace asuba ki dunga dubin shin alewansa (azzakari) yana mikewa to lafiyayen ɗa ne, tun yana jariri idan anka kula bayayin haka sati daya, sati biyu har zuwa wata to tabbas ɗanki na da matsala.

Kafin lokacin da kinka san ki daina masa wanka lafiyaye ne idan lokacin aurensa yazo mahaifinsa ya tambayeshi idan bazaki tambaye shi ba haka duk ɗa namiji yake wanda yake lafiyaye al’aurasa na miƙewa duk sanyin asuba.

Malama ta kara da cewa da tsohon namiji da yaro haka kowa yake Indai lafiya yake,matukar ya fara chanza to akwai matsala sai a nema a gyara.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post