Yanzu Yanzu An Tsinci Gawar Yar Shekara 14 Ta Mutu A Dakin Otal

 


Rundunar na ci gaba da bincike domin gano musababbin mutuwar yarinyar.


Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, yayin da yarinyar da suka kebe da saurayinta mai suna Lucky Okubo, a wani dakin otal da ke Yenagoa da niyyar biyan buĆ™atar juna. 


Rahotanni sun bayyana cewa yarinyar ta mutu ne sanadiyyar faduwa a bandaki. 


Faruwar hakan ke da wuya aka garzaya da ita zuwa Asibitin Tarayya (FMC) da ke Yenagoa, domin duba, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarta. 

An bayyana cewa kananan yaran biyu sun fara soyayya ne ‘yan watanni kafin faruwar lamarin.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post