Wanda ake zargin ta amince da gudanar da wannan sana’ar ta haramtacciyar hanya amma ta yi ikirarin cewa ta ba wa iyalan da ba su da ‘ya’yan nasu jariran, ba ga masu ibada ba.
Matan da aka ceto, masu shekaru tsakanin shekaru 20 zuwa 23, an yi musu sansani ne da nufin cinikin jariransu bayan an haife su.
Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar, Polycarp Nwonyi, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fatakwal a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu, ya ce ‘yan sanda sun kama Azoroh, mai kula da cibiyar safarar yara tare da wanda ke daure mata gindi a yayin samamen.
Wanda ake zargin ta amince da gudanar da wannan sana’ar ta haramtacciyar hanya amma ta yi ikirarin cewa ta ba wa iyalan da ba su da ‘ya’yan nasu jariran, ba ga masu ibada ba.