VIDEO: “An ɗaura auren saurayin da yaƙi karbar kamfani Gida Mota da Miliyan 20 don ya rabu da budurwar sa”


Rahotanni daga jihar Kano na cewa wani matashi mai suna Isyaku mai Baro ya ƙi yarda ya karɓi kyautar kamfanin buga ruwan Pure-Water da tsabar kuɗi Naira Miliyan 20 da kuma motar hawa ta kimanin Naira Miliyan 4 da ginanne gida a GRA Kano don ya rabu da Budurwar sa kamar yadda abokin karawar sa ya yi masa tayi.

Ku latsa nan don kallon Bidiyon

Alhaji Abubakar Mai Shadda wani hamshaƙin attajiri ne dake saffarar kaya daga Dubai zuwa Najeriya shine yaga yarinyar taje siyayya tare da ƙawayenta a ɗaya daga cikin kantunan sa a daren jiya inda yace yana sonta kuma ya nace yayin da shi kuma saurayin yarinyar sana’ar tura baro yake a kasuwar Kantin Kwari kuma gobe Juma’a za’a ɗaura musu aure da yarinyar.


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post