A shekarun baya-bayan nan an samu karuwar tsoffin taurarin fina-finan Hausa da ke fitowa fili suna neman taimako sakamakon matsalolin rayuwa da suka shiga ciki.
Masana na ganin akwai bukatar ‘yan masana’antar su hada kansu domin magance wannan matsala.
Jama’a da dama na mayar da martani kan yadda ake yawan samun tsofaffin taurarin fina-finan Kannywood da ke fitowa fili suna neman taimako sakamakon matsalolin rayuwa da suka fada a ciki.
Na baya-bayan nan shi ne yadda fitaccen dan wasan kwaikwayo na Hausa Abdullahi Shuaibu, wanda aka fi sani da Karkuzu, ya nemi jama’a su taimaka masa sakamakon lalurar makanta da yake fama da ita.
A wata hira da ya yi da Zinariya TV, ya bayyana cewa yanzu haka abinci na neman gagarar sa haka kuma tuni ya makance kuma ga shi ba shi da matsuguni.
Wannan lamari ya yi matukar jan hankalin jama’a a shafukan sada zumunta inda ake ta muhawara.
Hakan ne ma ya sa shahararren dan wasan kwallon kafa na Nijeriya Ahmed Musa ya ba shi naira dubu dariya biyar da yi masa alkawarin saya masa gida da ya kai na naira miliyan biyar.
Dalilin da ya sa taurarin ke yawan neman taimako
Masana da masu tsokaci kan harkokin Kannywood sun bayyana dalilai da dama da suke gani ke sa wa tsoffin taurarin fina-finan Hausa suke shiga mawuyacin hali da kan kai su ga neman taimako.
Dakta Muhsin Ibrahim, Malami a Cibiyar Nazari kan Afirka da ke Jami’ar Cologne ta kasar Jamus, ya shaida wa TRT Afrika cewa mawuyacin halin da ‘yan wasan Hausa ke shiga na da nasaba da abubuwa uku.
Rashin tsari
Malamin Jami’ar ya bayyana rashin tsari a masana’antar Kannywood a matsayin abu na farko da yake jawo wannan matsalar.
“Dama masana’anta ce da ake tafiyar da ita babu tsari, don haka babu wata kwantiragi da mutum ke sanya hannu idan zai yi fim ko wani tanadi alal misali da za a iya sakawa a wani asusu,” in ji Dakta Muhsin.
Ya kara da cewa: “Babu wasu tsare-tsare kamar na fansho yadda idan girma ya cimma mutum ko rashin lafiya ko mutuwa zai iya amfana ko iyalansa su amfana da wani fansho ko giratuti, baki daya babu wannan tsarin.”
Masanin ya ce ana tafiyar da masana’antar ne a tsarin ‘zo ka yi mini aiki na ba ka kudi’.
Rashin tanadi
Dakta Muhsin ya bayyana cewa a wannan bangaren ‘yan wasan na Kannywood sun rabu gida biyu.
“Wasu daga cikinsu da Allah ya yi musu daukaka sun samu kudi da yawa daga karshe sai su yi tunanin kamar wannan rayuwar za ta dore sai su ki tanadi.
“Da yawa kuma ba sa iya yin tanadi domin kuwa a gaskiya Kannywoo industry ce da yawanci kdin sayen abinci ake samu kawai. Shi ya sa lokacin da tauraruwarsu ta daina haskawa ko rashin lafiya ya same su ko girma ya cimma su, sai abubuwa su dagule,” in ji shi.
Rashin hadin kai
A cewar Dakta Muhsin, duk masana’antu wadanda suke da tsari da suka hada da makarantu ko bankuna ko kafafen watsa labarai ko ma’aikatu, akan samu rayuwa ta juya wa wani baya saboda asara ta rayuwa ko rashin lafiya.
“Idan akwai hadin kai, za a hadu ne a taimaka wa wanda irin wannan matsalar ta faru da shi, ba sai na waje ya ji ba. Amma saboda Kannywood ba su da hadin kai shi ya sa ba sa iya magance irin wadannan matsalolin sai an fito cikin duniya an sanar,” in ji shi.
Dakta Muhsin ya yi gargadin cewa akwai bukatar masu tasowa a harkar fim su koyi darasi kan wadannan abubuwan da ke faruwa.