Abin takaici an kama wannan matar mai suna Aisha Abubakar ta dauko har$a$hin b!ndigà sama da guda dubu biyu daga Abuja zata kaiwa bàra¥in dàji ma$u garkúwà da mutane a garin 'Yantumaki karamar hukumar Dan-Musa jihar Katsina
Kamar yadda zakuji matar ta fada da bakinta, tace wai yunwa ne ya sakata aikata wannan mummunan aiki, kuma wai shine karo na farko, akwai cikakken bidiyo na tambayoyin da aka mata tana amsawa a Telegram channel dina ta wannan
Amma ni ba zan taba yadda da uzurin yunwa ba, ace mutum saboda yunwa zai je ya aikata laifi mai muni irin wannan, wanda za'a ka$h£ 'yan uwansa da shi
Na sha fada, duk t@addànc!n da bara¥jn daji ke yi akwai gurbatattun mutanen a cikinmu da suke taimaka musu don kawai su samu kudi, don haka matsalar yaki da 'yan bind!ga ba wai laifin Gwamnati bane kadai, yanzu wannan da ace ta samu nasaran isar da alburusan ga '¥an b!ndiga Allah kadai Ya san barnan da za'ayi da su, don haka jama'a a cigaba da bawa jami'an tsaro hadin kai da bayanan sirri
Allah Ya sauwake, Ya kawo mana karshen wannan masifa