Gwamnatin Kano Ta Haramta Shirya Fina-finan Daba Da Harkar Daudu A Jihar

 

Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta haramta shirya fim ɗin da ke nuna fadan daba da harkar daudu a jihar. 

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne, ya bayyana hakan a yau jim kadan bayan wata tattaunawa da ya yi da masu shirya fina-finan Kannywood, suka hada da kungiyoyin MOPPAN, AREWA FILMS MAKERS, DIRECTORS da kuma PRODUCERS.

Shugaban ya ce biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da al’umma k eyi a kan shirya fina-finan da ke nuna fadan daba da harkar daudu a Jihar Kano, ya bayar da umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan da ke nuna fadan daba da harkar daudu a faɗin jihar.

Ya ce doka ce ta bai wa hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani fim da ta ke ganin ya ci karo da tarbiyya tare da al’adar al’ummar jihar.

Ya ce lokaci ya wuce da za a sanya ido ana shirya irin wannan gurbatattun fina-finai da ke kokarin lalata tarbiyyar yara.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post